Borno: Wasu Mata Sun Bukaci Sanin Makomar 'Ya'Yansu Da Mazajensu

Wasu mata da suka rasa mazajensu da 'yayansu maza sun yi kira ga gwamnatin jihar Borno da ta tarayya da su taimaka wajen gano ko sanar da su inda 'yayansu suke, ko a raye ko a mace.

Matan, da suka dauki hotunan mazajensu da 'yayansu, sun sanya bakaken tufafi a lokacin da suka yi wani taro a birnn Maiduguri don neman sanin makomar iyalansu.

A ranar 14 ga watan nan na Maris dai wasu mahara sun kai hari a wani barikin soja dake Giwa a garin Maiduguri, inda suka yi awon gaba da wasu fursunoni mambobinsu. Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun bude masu wuta kuma wasu sun mutu sakamakon haka. Dalili kenan da matan suka fara jefa alamar tambaya akan makomar 'yayansu.

Hauwa Bala na daga cikin matan dake yin kiran ga hukumomi, ta ce shekara 7 kenan rabonta da mai gidanta kuma ba ta da mai taimaka mata. Hauwa ta ce sojoji ne suka kama mai gidanta a lokacin da suka kai wani samame.

Ita ma Hauwa Mohammed ta yi kira ga gwamnati da ta tallafa masu saboda yanayin da suka sami kansu a ciki.

A baya bayan nan dai kwamnadan rundunar sojan Lafiya Dole, Olusegun Adeyimi, ya bayyana cewa a shirye suke su saki duk wani da ke hannunsu bayan an tabbatar da cewa ba shi da laifi. Kwamandan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da rundunar ta wanke wasu mayaka su 982.

Ga cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Borno: Wasu Mata Sun Bukaci Sanin Makomar 'Yayansu Da Mazajensu