BORNO: Kone-konen Boko Haram Sun Jawo Fari da Yunwa

Borno Kone-Konen

Kone konen da kungiyar Boko Haram ta dinga yi a jihar Borno sun sa jihar ta shiga wani halin fari na bazata da yunwa saboda baicin karuwar kwararowar hamada yawancin jama'ar jihar basu iya fita zuwa noma ba

Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya wadda ta kasance mahaifar kungiyar Boko Haram ta kwashe fiye da shekaru biyar tana cikin mugun azabar kungiyar ta'addancin.

A duk cikin jihohin arewa maso gabas jihar Borno ce ta fi fama da hare-hare da kone konen da 'yan Boko Haram suka haddasa.

Bayan sun kwace garuruwa da dama sun kashe dubban mutane, sun lalata muhallai sai kuma suka shiga kone kone. Hatta sansanonin da aka samar ma wasu masu gudun hijira lokacin da rikicin ya fara basu tsira ba.

Yawancin sassan jihar Borno sun yi shekaru hudu ko fiye babu damar yin noma sanadiyar rashin tsaro, sace sace da kashe kashen mutane da kungiyar ke yawan yi.

Sau tari dan abincin da ya rage a wasu wuraren kungiyar na bi tana sacewa kana ta kone kauyukan bayan ta kashe na kashewa ko kuma wasu sun samu sun arce. Kungiyar ta sa jihar dake kusa da hamada fadawa cikin wani halin kunci

Ga bidiyo da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

BORNO: Kone-konen Boko Haram Sun Jawo Fari da Yunwa

DOMIN KARIN BAYANI

Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n

Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU