Bom Ya Kashe Akalla Mutane 6 A Mogadishu

A kalla mutane goma sha biyu suka mutu, sama da ishirin, kuma suka ji rauni, lokacin da wata mota, da aka dankarawa boma-bomai ta tarwatse yau alhamis, a kofar wani gidan cin abinci a babban birnin kasar Somaliya.

Shaidu, sun gayawa Sashen Somaliya, na Muryar Amurka, cewa, fashewar, ta auku ne, a kofar wani gidan cin abinci, dake kan hanyar Maka Al-Mukarama, dake wani titi, da aka fi samun hada-hadar, jama’a a Mogadishu.
Rufin gidan cin abincin, ya rufta da mutane, da dama a ciki, inji wani shaida, da ya nemi a sakaya sunan sa.

Hukumomin motar daukar marasa lafiya masu bukatar agajin gaggawa, sun ce a kalla, mutane shida, da suka ji rauni, a fashewar sun mutu, a kan hanyar zuwa asibiti.