Shugaban kungiyar kwadagon Kwamred Ayuba Wabba ya bayyanawa Muryar Amurka dalilin janye yajin aikin.
Yace koda suka shiga yajin aikin mutane da dama sun nemi su sa baki domin a samu sasantawa da zummar mayar dasu kan teburin shawara. Yace 'yan majalisun tarayya da kuma shugban jam'iyyar APC Ahmad Bola Tinubu wanda har ofishinsu ya je duk sun sa baki.
Kiran da Bola Tinubu da 'yan majalisun tarayya suka yi masu na cewa su nemi hanyar sasantawa ya sa suka duba suka yanke shawarar janye yajin aikin.
To saidai a ganin wasu, yajin aikin bai samu cikakkiyar nasara ba domin wasu ma'aikata, da suka hada da ma'aikatan man fetur, sun bijirewa yajin aikin.
Masu sharhi,, irinsu Hassan Gimba Ahmad yace duk lokacin da kungiyar kwadago ta kira yajin aiki, yakamata a ce ma'akaci ya amince da hakan. Amma idan ma'aikaci yaki ya fita yajin aiki, to bai yadda dasu ba, kuma ya kamata su duba menene ya jawo hakan.
Hassan Ahmad Gimba yace, na farko, mutane sun dade suna tunanen shugabannin kungiyar kwadago suna anfani da jama'a su gina kansu ne, domin duk lokacin da sai kungiyar ta tilastawa mutane su shiga yajin aiki, to ko basu fahimci shugabannin ba ko kuma basu yadda dasu ba.
Shi dai Bola Tinubu, ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi gwamnoni da ministoci zuwa hedkwatar kungiyar kwadagon. Yayi jawabi na zawarci domin shawo kan kungiyar.
Sakataren tsare-tsaren kungiyar kwadagon, Kwamred Nuhu Abayi Toro yace zawarcin wata 'yar manuniya ce. Yace zawarcin na jigajigan kungiyar APC, ta nunawa 'yan Najeriya, cewa kungiyar kwadago tana bisa hanya, domin ta tabbatar an yi adalci a Najeriya.
Ga karin bayani..
Your browser doesn’t support HTML5