Tun farko dai mayakan na Boko Haram sun kai wa jami’an sojan dake garin Marte hari, inda suka halaka wasu sojoji tare da kwace motoci da kayakin yaki daga jami’an sojan.
A cewar wasu da suka tsallake rijiya da baya a garin Marte, mayakan sun afka wa barikin soja suka yi kone-kone tare da kashe sojoji, kuma a cikin garin Marte ma an kone wasu wurare masu yawa.
Wannan shi ne karo na farko da Boko Haram ta kai hari tare da kwace ikon gari tun nada sabbin hafsoshin tsaron Najeriya, da yanzu haka ke ci gaba da yin aiki a wasu bangaren kasar dama dajin Sambisa.
Lokacin da sabbin hafsoshin soja suka kai ziyara jihar Borno a karon farko, gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya ba su shawara cewa ya kamata sojoji sun ankara, cewa idan suna yaki da 'yan ta’adda a arewacin Borno mayakan na yin kaura ne zuwa dajin Sambisa. Haka zalika da zarar an sake afka musu a dajin Sambisa, sai su sake komawa arewacin jihar.
Mallam Aliyu Usman mai kula da harkokin tsaro, ya bai wa gwamnatin Borno shawarar sake duba shirinta na sake mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu na asali, ganin yadda har yanzu ake ci gaba da fama da ‘yan ta’adda.
Batun sake karbe ikon garin Marte ya tayar wa da al’ummonin yankin arewacin jihar hankali, wadanda ba da jimawa ba suka sake komawa garuruwansu domin ci gaba da rayuwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5