Boko Haram Ta Kashe Mutane Biyu Kan Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa.

Sojojin Najeriya suke nuna tutar Boko Haram da suka kwace.

Sojojin Najeriya suke nuna tutar Boko Haram da suka kwace.

Sun kai harin ne a wani kauye da ake kira Dalwa kilomita 30 daga birnin Maiduguri,kamar yadda kwamishinan 'Yansandan jahar ya fada.

Rundunar 'Yansanda ta jahar Barno ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, sakamakon harin kwanton bauna da wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai kan tawagar motoci dake bi ta kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Kwamishinan 'Yansanda na jahar Damien Chukwu ne, ya shaidawa manema labarai aukuwar lamarin a wani taro da ya kira a maraicen Talata.
Kwamishina Damien yace jami'an sandan kwantar da tarzoma su shida sun jikkata, sakamakon harbin-kan-mai-uwa-da-wabi da 'yan bindigar ta Boko Haram suka auna kan ayarin motoci da jami'an tsaro suke yiwa rakiya kan wannan hanya. 57 sun tsallake rijiya da baya. Kuma babu makaminsu ko daya da ya bata.

Su dai 'Yansandan, suna cikin wata motar fasinja mai kujeru 80 mallakar gwamnatin jahar Barno, kuma tana jigilar 'Yansandan ne zuwa yankin Askira-Uba domin aikin tsaro. Wadanda suka jikkatan an kai su asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri inda ake yi musu jinya.

Cikin ayarin har da motar da take dauke da gawar wata jami'ar 'yansanda wacce Allah Ya yiwa cikawa, motar gawar,inji Kwamishina Damien, ta tsallaka, amma 'yan rakiya sun watse, amma yanzu sun fara fitowa daya bayan daya.
Cikin wadanda suka mutu harda saje Bala, da kuma matukin wata babbar motar dakon kaya, wacce take dauke da magunguna domin 'yan gudun hijira.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram ta kai hari kan hanyar Damboa