Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi Lawan Bukar, wanda shine Darektan Majalisar Koli ta Sadarwa a Jihar Diffa.
“Lallai gwamnati ta tabbatar da cewa an samu rikici a dajin Dosso misalin kilomita 30 a garin da ake cewa Karanga. Wato lallai gwamnati ma ta bayyana cewa anyi rikicin amma, a takaice sai dai a yanzu babu wanda zai iya ce maka ga abunda ya wakana”, a cewar Mr. Bukar.
Ya kara da cewa “amma har yanzu gwamnati bata fito ba tace ga adadin barnar da aka samu, ko kuma su ‘yan Bokon, ga wadanda aka kashe. Yanzu kowa yana jita-jitan abunda ya faru, kuma kowa yana jiran sakamakon da gwamnati zata fidda.
Lawan Bukar ya kara da cewa jama’a hankulansu ya tashi, musamman ma gani kamar rigingimun Boko Haram din sun zo karshe.
“Gaskiya a yanzu, a Diffa yanda mutane suke magana, domin kowa tsammani yake kamar an kare, yanzu dai kawai abunda mutane suke bayarwa, karfin gwiwa ne suke baiwa jami’an tsaro, yadda dai kar ayi sake su cigaba da irin wannan abunda suka yi na fari.
A halin yanzu dai Shugaban Nijar, Muhammadou Issoufou ya gudanar da taro da hafsoshin tsaro domin tattauna lamarin.
Your browser doesn’t support HTML5