Boko Haram Ta Fi Anfani da Yara Mata Wajen Aiwatar da Harin Kunar Bakin Wake

Harin kunar bakin wake.

Sakamakon binciken da sojojin Amurka suka gudanar akan yawaitar hare haren kunar bakin wake da Boko Haram ke kaiwa cikin 'yan kwanakin nan na nuni da cewa 'yan ta'addan sun fi anfani da yara mata aiwatar da aika aikarsu

Binciken ya nuna cewa cikin hare haren kunar bakin wake 434 da kungiyar Boko Haram ta aiwatar 'yan yara mata kanana ne suka kai guda 244.

Dangane da wannan yin anfani da yara mata ita ma hedkwatar sojojin Najeriya ta bakin kakakinta Birgediya Sani Kukasheka ta tabbatar cewa wasu iyaye ma kan bada 'ya'yansu wa kungiyar Boko Haram domin yin anfani dasu wajen kai harin kunar bakin wake.

A farkon watanni bakwai na wannan shekarar kimanin 'yan yara mata tamanin ne suka rasa rayukansu a sashen arewa maso gabas sanadiyar kai harin kunar bakin wake.

Dangane da dalilin da ya sa 'yan Boko Haram suka fito da salon yin anfani da yara mata kanana wajen kai harin kunar bakin wake, Hajiya Halima Baba Ahmed mai fafutikar kare 'yancin mata a Najeriya tace su 'yan Boko Haram na ganin ba za'a taba tsammanin yara mata zasu aikata irin wannan abun ba. A nasu tunanen babu wanda zai kyautata zaton yara mata zasu fada hannun su har su yi anfani dasu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Ta Fi Yin Anfani da Kananan Yara Mata Aiwatar da Harin Kunar Bakin Wake - 2' 22"