Boko Haram Ta Dauki Alhakin Harbo Jirgin Saman Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

Wani hoton mayakan Boko Haram (AFP).

A ranar Laraba 31 ga watan Maris jirgin saman Najeriyar ya yi batan dabo, bayan da ya kauce daga kan na’urar da ke bibiyar zirga-zirgar jiragen sama.

Kungiyar mayakan Boko Haram, ta yi ikrarin cewa ita ta kakkabo jirgin saman sojin Najeriya da ake ta nema.

Kungiyar ta Boko Haram ta fitar da sanarwar ta ta ne a wani bidiyo mai tsawon kusan minti takwas a ranar Juma’a, inda aka nuna mayakanta suna tafiya a wata hanya dauke da makamai.

Bidiyon har ila yau ya nuna yadda jirgin ya kama da wuta a sama kafin daga bisani ya fadi, inda a karshensa aka ga wasu daga cikin mayakan suna hawa kan tarkacen jirgin.

Hakazalika, bidiyon ya nuna gawar wani soja a cikin baraguzan jirgin da ya fadi.

Karin bayani akan: Boko Haram, Jirgin Yakin Saman na Najeriya, jihar Borno​, Sojojin Najeriya, Nigeria, da Najeriya.

Wata sanarwa da rundunar sojin saman Najeriyar ta fitar a ranar Juma'a, ta ce akwai alamu da ke nuna cewa jirgin nata faduwa ya yi a yankin jihar Borno, amma ba ta ba da wata hujja ba.

Sojojin Najeriyar sun bayyana cewa dakarunta biyu ne a cikin jirgin mai lamba NAF 475.

“Matuka jirgin sun hada da Flight Lieutenant John Abolarinwa da Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele.” Sanarwa da rundunar sojin saman Najeriyar ta fitar a shafin Twitter dauke da sa hannun darektan yada labarai, Air Commodore Edward Gabket ta ce.

Jirgin na daga cikin jiragen yakin Najeriya da ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, a yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Najeriyar ba ta mayar da martani kan ikrarin na Boko Haram ba.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu:

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Ta Dauki Alhakin Harbo Jirgin Saman Najeriya - 1'20"