Abokin aiki Yusuf Harande ya samu ya zanta da Danladi Ahmadu wanda yace yana yiwa Boko Haram wasu ayyuka.
Akan rasuwar shugaban kungiyar Shekau, Danladi musanta ikirarin ya kuma ce shugaban yana nan da rai.
Inji Danladi suna neman a kawo karshen rikicin lafiya. Shugaban kasa ya samu lafya su ma su samu lafiya. Suna bukatar shugaban kasar Chadi ya shiga tsakaninsu da gwamnatin Najeriya domin a kawo karshen rikicin. Shugaban Chadi ya karbo masu hakinsu daga shugaban Najeriya.
Akan sakin yaran Chibok Danladi yace akwai wasunsu da aka kashe 'yanuwansu. Wasu sun yi asarar shaguna da gidaje. Wasu an hanasu matsayi. Idan aka daidaita duk wadannan alamura za'a sako 'yan matan. Sabili da haka sai an zauna kowa ya fadi abun dake zuciyarsa kafin a samu masalaha.
Dangane da 'yan matan Chibok da suke tsare dasu Danladi yace suna nan lafiya. Suna ci suna sha. Yace dama can basu iya karau ba ne amma yanzu sun iya. Yace suna nan cikin koshin lafiya. Ya musanta zargin cewa ana yiwa yaran wasu abubuwa da basu dace ba.
Suna bukatar gwamnatin Najeriya da na Chadi su zauna dasu a samu lafiya da kwanciyar hankali. Danladi yace abubuwan da ake yi a Najeriya ba kungiyarsu ke aikatasu ba. Barayi da wasu bata gari da suka hada da wasu sojoji ke yinsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5