Boko Haram: Janyewar Sojojin Chadi Ta Sa Mutanen Damasak Gudu Barin Gari

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan Boko Haram da sojojin Chadi su ka kama kwanan baya

Yayin da 'yan Boko Haram ke kara tayar da kayar baya cikin 'yan kwanakin nan, mutanen garin Damasak sun gudu saboda sojojin Chadi masu kare su sun janye.

Tsoron yiwuwar harin Boko Haram ya sa kowa ya yi ta kansa a garin Damasak, bayan da sojojin Chadi su ka janye daga garin.

Wani dan garin mai suna Malam Umaru ya shaida ma wakilinmu Haruna Dauda cewa hatta tsofaffi sun gudu sun bar garin kuma kowa ya sha alwashin ba zai dawo ba sai gwamnati ta tura sojoji madadin na Chadin da su ka koma kasarsu. Ya ce dama abin da ya sa su ka dawo shi ne bayan da sojojin Chadi da na Nijar su ka kwato garin daga ‘yan Boko Haram sai su ka ce ma su tunda babu ‘yan Boko Haram sai su dawo, tare da ba su tabbacin kariya.

Malam Umaru ya ce ana nan sai sojojin da su ka rage a garin wato sojojin Chadi su ka tara shugabannin garin su ka gaya masu cewa su je su gaya ma hukumomin Najeriya cewa za su tashi saboda haka a tura sojojin Najeriya zuwa wurin. Y ace da jin haka sai dattawan garin su ka je Maiduguri su ka yi ta jiran ganin gwamna har kwanaki sama da biyu. Don haka sai su ka koma Damasak, al’amarin da ya sa ‘yan garin su ka yi ta gudu su na barin garin saboda ganin yadda ‘yan Boko Haram su ka yi ta barna a garin a baya.

Ya ce ‘yan Boko Haram na tsoron sojojin Chadi saboda a baya sun yi niyyar shiga garin amma bas u ji da dadi ba saboda jajircewar sojojin na Chadi wadanda a lokacin su ka fatattaki ‘yan Boko Haram har su ka yi ta gudu sun a barin kayakinsu.

Your browser doesn’t support HTML5

DAMASAK - 4'28''