Gamayyar kungiyoyin sa kai sun kuduri aniyar saka ido akan yadda za a yi amfani da kudaden da kuma kayakin tallafin da aka samo daga gwamnatoci da kungiyoyi da sauran hukumomi a ciki da wajen Najeriya don tayar da komadar mutanen da hare-haren Boko Haram su ka rutsa da su har su ka tagayyara a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari y ace kungiyoyin na rajin kare muradu daban-daban ne na dan adam, amma sai su ka fahimci cewa kowaccensu ta dama da wahalhalun da mutanen arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta. Don haka su ka yake shawarar yin hadakar ta kare mutanen.
Kungiyoyin goma, sun fito ne daga Bauchi da Taraba da Gombe da Yola da Adamawa da Borno da Yobe da Kano. Kwamrad Sa’idu Kabiru Dakata na cibiyar “Center For Information Technology and Development “ ya fayyace ra’ayinsu game da yadda su ke ganin ya kamata a kashe kudaden da cewa kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa da zummar amfani da shi wajen kashe Naira biliyan biyar wajen tallafa ma wadanda ‘yan Boko Haram su ka tagayyara, bai kamata a bashi kudin kai tsaye ba, ya kamata a tsara yadda za a kashe kudaden a baiwa kwamitin ya yi amfani da shi don gudun kashe kudaden ta hanyar da ba ta dace ba. Y ace bangaren ilimi ne ya kamata ya fi sauran amfana. Shi kuwa Mohammed Wuyo na kungiyar “Borno Coalition of Democracy and Progress” ya ce shi ma a ba da muhimmanci ga gyara makarantu da sauran abubuwan da su ka shafi ilimi. Hasalima, akasarin ‘yan kungiyar so su ke a baiwa fannin ilimi fiyayyen muhimmanci.
Gamayyar kungiyoyin sa kai sun kuduri aniyar saka ido akan yadda za a yi amfani da kudaden da kuma kayakin tallafin da aka samo daga gwamnatoci da kungiyoyi da sauran hukumomi a ciki da wajen Najeriya don tayar da komadar mutanen da hare-haren Boko Haram su ka rutsa da su har su ka tagayyara a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari y ace kungiyoyin na rajin kare muradu daban-daban ne na dan adam, amma sai su ka fahimci cewa kowaccensu ta dama da wahalhalun da mutanen arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta. Don haka su ka yake shawarar yin hadakar ta kare mutanen.
Kungiyoyin goma, sun fito ne daga Bauchi da Taraba da Gombe da Yola da Adamawa da Borno da Yobe da Kano. Kwamrad Sa’idu Kabiru Dakata na cibiyar “Center For Information Technology and Development “ ya fayyace ra’ayinsu game da yadda su ke ganin ya kamata
Kwari reports that the NGOs’ involved protect various interests but share the common pains of the people of the North East, particularly those directly affected.
Your browser doesn’t support HTML5