Boko Haram Bata Kafa Tutarta Ba a Koina – Janar Irabor

Sojojin dake yaki da mayakan Boko Haram

Manjo Janar Lucky Irabor ya musanta zargin cewa kungiyar Boko Haram ta kafa tutarta a wani wuri tsakanin Najeriya da kasar Kamaru

A hirarsa da wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, kwamandan sojojin hadin gwuiwa na kasashen yankin tafkin Chadi, Manjo Janar Lucky Irabor, ya musanta zargin cewa Boko Haram ta kafa tuta a wani zirin dake tsakanin Najeriya da Kamaru.

Inji shi, kwana kwanan nan ya je kasar Kamaru kuma ya zagaya duk wararen da sojojinsu suke, kuma babu wani abu makamancin hakan.

Janar Irabor ya amince cewa akwai burbudin mayakan Boko Haram har yanzu, sai dai ya ce karfinsu ya ragu ainun. Sojojin zasu ci gaba da yaki dasu har sai sun ga bayansu, injishi. Haka kuma Kwamandan ya ce yanzu haka mayakan Boko Haram suna mika wuya saboda matsin da suke samu daga kasashen tafkin Chadin.

Amma Dr Saleh Abba, likitan wata kungiya dake kula ‘yan gudun hijira, ya ce har yanzu mutane sun kosa saboda ana ci gaba da harbe-harbe kuma ‘yan ta’adan ke tada kauyuka. Kazalika ana ci gaba da tare hanyoyi da sace mutane.

Ga rahoton Hassana Maina Kaina da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Bata Kafa Tutarta Ba a Koina – Janar Irabor - 2' 39"