BOKO HARAM: ‘YAN MAJALISA DAGA AREWA MASO GABAS, NA NEMAN DAUKIN FARFADO DA YANKIN
‘Yan Majalisun Dattawa da na Wakilai daga Arewa maso gabashin Najeriya sun kammala shirinsu na gabatar da kudurin doka na bai daya na farfado da yankin ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa. ‘Yan majalisun da su ka fito daga jahohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Taraba da Bauchi, na so ne a sake gina yankin ta wajen sake tsugunar da mutanen da Boko Haram ta watsar da sake gina hanyoyi da makarantu da harkokin kasuwanci da dai sauransu, wadanda su ka durkushe ko lalace sanadiyyar rikicin Boko Haram.
Wakilin Muryar Amurka a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito ‘yan majalisar na cewa kudurin dokar bai dayan da za su gabatar zai tanaji kafa wata hukuma ta musamman ta sake farfado da yankin. Sanata Marafa Bashir Abba mai wakiltar yankin Taraba ta Tsakiya y ace Sanata Danjuma Goje ne Shugaban wannan yinkurin kuma hukumar da su ke so a kafa kwatankwacin ta NDDC ce da ke yankin Naija-Delta (Niger-Delta).
Sanata Abba y ace an sha wahala sosai a yankin saboda da haka ya kamata gaggauta yankin. Wannan ya zo daidai da ra’ayin Mr. Adamu Kamale, mai wakiltar Madagali da Machika a Majalisar Wakilai y ace har an yi nisa a wannan yinkurin. Kuma y ace duk wani batun cigaba da za a kawo a yankin zai wanzu zuwa karkara. Su ma kingiyoyi masu zaman kansu sun yi na’am da wannan hobbasar.
Your browser doesn’t support HTML5