Da safiyar yau Laraba ne mutanen garin Dapchi suka ga wani abu mai kamar almara da ba a taba garin irinsa ba, inda ‘yan kungiyar Boko Haram suka mayar da ‘yan matan da suka sace ga iyayensu.
A yau ne ‘yan kungiyar iyayen yaran garin Chibok suka shirya kai ziyara ga iyayen ‘daliban garin Dapchi, inda suka gayyaci ‘yan jarida zuwa garin, wadanda daga bisani suka ci karo da wannan lamari, har ta kai ga jami’an tsaro sun taka musu birki da hanasu shiga cikin garin Dapchi.
A wata sanarwa da ofishin Ministan labaran Najeriya, Lai Mohammad ta fitar ta ce an sako matan ne da taimakon wasu kasashe abokan Najeriya ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
Wasu daga cikin iyayen ‘yan matan sun tabbatarwa da Muryar Amurka cewa ‘yan Boko Haram cikin motoci ne suka mayar da ‘yan matan da safiyar yau Laraba.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5