BMO Mai Goyon Bayan Shugaba Buhari Tace Shugaban Bai Niyar Tazarce

Shugaba Muhammadu Buhari

Wata kungiya mai goyon bayan shugaban Najeriya dake kiran kanta “Buhari Media Organsation” (BMO), tace shugaba Muhammadu Buhari bai yanke wata shawarar yin tazarce ba

A wata sanarwa da shugaban kungiyar BMO Niyi Akinsiju ya sanyawa hannu a Abuja na cewa masu gangamin yin tazarcen su girmama shugaban kasa kuma su daina wannan gangamin.

Akinsiju ya fada cewa kungiyarsa na ran cewa kalaman na shugaban kasar zai kawo karshen wannan labarin kanzon kurege baki daya.

Kungiyar ta BMO ta fada cewa wannan sanarwar da shugaban kasa ya yi cewa bashi da wata niyar shiga takara a karo na uku matsayinsa ke nan saboda haka, ‘ya yi kira ga yan Najeriya su yi watsi da kiran da wasu ke yi na sauya dokar wa’adin shugabanci, lamarin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Shi kuwa Awala Rafsanjani dan rajin kare hakkin bil adama a Najeriya, yace ganin irin alkawuran da shugaba Buhari ya dauka a baya cewa zai yi takarar shugabancin kasa sau daya amma kuma ya sauya tunaninsa ya nemi wa’adi na biyu, akwai yiwuwar wannan batun tazarcen ya zama gaskiya.

Sai dai yace dole ne ‘yan Najeriya su tashi haikan su bayyana rashin amincewar su da kakkausar lafazi kana su tabbatar da ganin cewa, sun kare ‘yancinsu.

Rafsanjani ya yi fashin bakin ne a wata hira da babbar editar Muryar Amurka Alheri Grace Abdu,

Saurari hirar:

Your browser doesn’t support HTML5

RAFSANJANI A KAN TAZARCEN BUHARI