Bisa Alamu Mutanen Iran Ba Zasu Yi aikin Hajjin Bana Ba

Rouhani, shugaban Iran

Kasar Iran da Saudiya sun kasa cimma matsayi akan aikin hajjin bana saboda haka 'yan Iran ba zasu samu zuwa hajji ba bana

Kamfanin dilancin labaran kasar Iran da ake kira IRNA a takaice, yace domin kasar da Saudiya sun kasa cimma daidaito 'yan Iran ba zasu yi aikin hajjin bana ba.

Kamfanin ruwaito Ali Jannati ministan harkokin addini da al'adu na kasar na cewa kasarsa ta dauki wannan matakin ne saboda halayen da kasar Saudiya ta nunawa tawagar wakilan kasar Iran da suka je Saudiya domin tattauna ka'idodin aikin hajjin na bana.

To saidai a bangaren Saudiya, cewa tayi bukatun da kasar Iran ta gabatar mata basu yiwuwa.

Tun farko kafofin yada labarai na kasar Saudiya suka ce wakilan Iran sun bar kasar ba tare da cimma ko kulla wata yarjejeniya ba.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta samu rauni bayani da 'yan kasar Iran dari hudu suka rasa rayukansu a lokacin aikin hajjin bara