Birtaniya Zata Mayar Wa Rasha Martani

Firayim Ministar Birtaniya,Theresa May

Da zara an tabbatar cewa Rasha na da hannu a yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asiri dan asalin Rasha da diyarsa, da yanzu suka zama 'yan Birtaniya, Firayim Ministar Birtaniya Theresa May ta sha alwashin mayar da martani

Firayim ministar Bitrtaniya, Theresa May, tayi alkawarin daukar matakin da ya dace domin mayar da martani, muddin aka gano cewa Rasha ce ke da alhakin sa wa wani tsohon dan leken asirin Rasha da diyarsa guba.

‘’Amma bari kar muyi riga malam masallaci, bari mu ba ‘yan sanda lokaci, da kuma damar gudanar da dukkan binciken da ya dace" in ji firayim ministar a lokacin da take magana da gidan telebijin na ITV jiya alhamis. ‘’Ba shakka idan ta kai na a dauki mataki, gwamnati ba zata yi kasa a guiwa ba, zamu yi hakan a lokacin da ya dace, wannan kuma zai dogara ne akan irin kwararan hujjojin da muke dasu’’.

Sakatariyar Harkokin cikin gidan Britaniya, Amber Rudd, ta shaidawa majalisar dokoki cewa, ‘’Amfani da iskar guba mai lalata jijiyoyin jikin bil Adama, babban laifi ne na ganganci a Britaniya. Wannan yunkurin yin kisa ne ta muguwar hanya cikin bainar jama'a."

Wani Jami'in ‘yan sanda ya fadawa kafar yada labarai ta SKY NEWS cewa adadin mutane 21 ne suka samu rauni sakamakon shakar wannan mugun sinadarin da aka baza shi kusa da wani shagon sayar da kaya a birnin Salisbury na kudancin Britaniya.

Har yanzu wasu mutane 3 suna asibiti, watau mutumin da a bisa dukkan alamu aka nemi kashewa, tsohon mai leken asiri na kasar Rasha Sergei Skripal, da diyar sa Yulia, da wani dan sandan kasar Birtaniya Nick Bailey wanda yayi kokarin taimaka musu bayan ya fahinci cewa sun yanke jiki sun fadi ba cikin hayacinsu ba.

Wani wanda yaga abinda ya faru ya fada wa wani dan jaridar kasar Birtaniya cewa Yulia Skripal ta some, bakinta na kumfa, kuma idonta a bude, amma ya kafe. Ya ce shi kuma mahaifin nata, ya sandare, hannuwansa ba su iya motsi, idonsa na kallon wuri guda ba ya motsi kamar matacce.

Shi dai Skripal da diyarsa har zuwa yammacin jiya alhamis ba su cikin hayyacin su, Shi ma Bailey yana cikin mawuyacin hali, amma an ce idonsa biyu yana iya gani.