A yau Laraba ne Firaministan Birtaniya Theresa May, za ta fuskanci kuri’ar yanke kauna, ko kuma akasin hakan daga ‘yan majalisun jam’iyyarta masu ra’ayin rikau.
Wannan shi ne lamari na baya-bayan nan dangane da yadda take tafiyar da shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.
Idan har ‘yan majalisu dake da rinjaye suka kada kuri’ar yanke kauna ga Firaminista May, to ya zama dole ta yi murabus daga matsayinta na firaiminista.
Idan kuma ta iya tsallake kuri’ar, ba za’a sake kada irin wannan kuri’ar ba har sai bayan shekara daya.
May, ta sha alwashin sai ta ga abun da ya turewa buzu nadi akan wannan yunkurin na ficewar kasar daga kungiyar, tana mai cewa sauya shugabanci a wannan lokacin, ka iya wargaza yunkurin ficewar kasar daga kungiyar Turai.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar adawa ta Labor Party, Ian Lavery ya fitar, ya ce rashin iya shugabancin na May, ya kara jefa kasar cikin halin da take ciki.
A hukumance, ranar 29 ga watan Maris din shekarar 2019, ita ce ranar karshe da Birtaniyan ya kamata ta fice daga kungiyar.