A wani jawabi da ba kasafai aka saba gani ba, Shugaban hukumar tattara bayanan sirrin cikin gida na Birtaniya, ya ce bai taba gani barazanar ta’addanci da kasar ke fuskanta ta yi muni ba fiye da yanzu a iya shekaru 34 da ya kwashe yana aiki.
“Abu ne da ya fito karara cewa muna fuskantar barazanar ‘yan ta’adda masu tsananin kishin Islama. Wannan barazanar na da fuskoki da dama, tana bayyana a hankali akan wani mizani da bamu taba gani ba, amma kuma mu ma ta irin wannan salo mu ke mai da martani.” In ji shugaban hukumar ta MI5, Andrew Parker.
Ya kuma kara da cewa, sun lura da wani irin bunkasa da barazanar ta yi a wannan shekara, inda aka kashe mutane 36 a hare-hare daban-daban a Biranen London da Manchester.
“Akalla hare-hare 20 muka dakile cikin shekaru hudun da suka gabata, kuma da an dakile wasu da dama da irin matakan gaggawa da muke dauka tare da ‘yan sanda”, a cewar Parker.
A watan da ya gabata ma, wani karamin bam na hadin gida ya raunata akalla mutane 30, wannan hari shi ne na biyar da ‘yan ta’adda suka kai a Birtaniya a bana.