Birtaniya, Jamus Sun Yi Kira Da A Tsagaita Wuta A Gaza

  • VOA

Gaza

Ministan harkokin wajen Birtaniya Daivd Cameron da takwararsa ta Jamus Annalena Baerbock sun yi kira ga tsagaita bude wuta ta dindindin a Gaza a wata sanarwar hadin gwiwa da aka buga a jaridar Birtaniya ta Sunday Times.

"Duk mu yi iya bakin kokarin mu wurin samar da shirin tsagaita wuta ta dindindin, da zai kai ga zaman lafiya mai dorewa," in ji jami’an diflomaisyar biyu. "Samar da haka cikin gaggawa nada muhimmanci kuma ana bukatar hakan nan da wuri."

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fada a wata sanarwa yau Lahadi cewa ajiya Asabar ma’aikatanta masu aiki karkashin shirin kiwon lafiyar MDD a asibitin Shifa dake arewacin Gaza sun taimaka wurin kai kayayyakin aiki da suka hada da na’urori daban-daban da magunguna.

FILE PHOTO: WHO-led humanitarian assessment team visits Al Shifa Hospital in Gaza

WHO ta ce asibitin baya aiki sosai, kana yana fama da karancin ma’aikata da likitoci da ma’aikatan nes da ma ma’aikatan sa kai wanda adadin su bai haura 70 ba.

Hukumar lafiyar ta duniya ta ce dubun dubatar mutane da suka rasa matsugunansu ne suke zama a cikin ginin asibitin da ma karkashin ginin.

Displaced Palestinians gather in the yard of Gaza's Al-Shifa hospital on December 10, 2023, as battles continue between Israel and the militant group Hamas in the Palestinian territory.

Ma’aikatar Sojin Isra’ila ta fada yau Lahadi cewa dakarunta a Jabalia sun gano wata kofa a cikin dakin wani yaro dake kai ga ramin da mayakan Hamas ke ciki. An watsa bidiyon kofar da aka gano a kan yanar gizo.

Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a wani taron manema labarai ta telbijin a ranar Asabar cewa kashe ‘yan Isra’ila uku da aka yi garkuwa dasu da sojojin Isra’ilan ne suka kashe su bisa kuskure a ranar Juma’a, ya tayar masa da hankali haka ma ya tada hankalin kasar baki daya.

2023 in photos: Israel-Hamas war

Netanyahu ya kira yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas a matsayin yaki mai wanzuwa wanda dole ne a gwabza har sai an samu nasara, duk da matsin lamba da asarar da za a yi, ya kara da cewa za a kawar da ayyukan soja a Gaza kana za ta kasance karkashin ikon tsaron Isra'ila.