Firai ministan Britaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, ba'a yi gaggawa ba idan an fara shirin farfado da tattalin arzikin kasar bayan COVID-19, in da a yau Talata ya sanar da kashe sama da dala biliyan goma sha bakwai a tsarin ilimin kasar da kuma miliyan dubu shida da dari da talatin kan kayayyakin more rayuwa.
Da yake jawabi a kwalejin fasaha ta Dudly da ke tsakiyar birnin London, Johnson ya ce za'a ga kamar riga mallam masallaci ne magana a kan abinda za'a yi bayan wucewar CODVID, bisa la’akari da yadda cutar ta ke kara habaka a kasar, da kuma wadansu kasashe da dama na duniya.
Sai dai yace Birtaniya ba za ta ci gaba da zama fursunan cutar ba.
Johnson wanda ya kwatanta shirin nashi da na tsohon shugaban kasar Amurka Franklin D. Roosevelt mai lakabiN “New Deal”, da tsohon shugaban na Amurka ya gabatar a shekarar 1930, da nufin zaburar da tattalin arzikin kasar bayan mummunan komadar tattalin arzikin da kasar ta fuskanta, ya yi alkawarin ci gaba da gina kasar da kuma hanzarta aiwar da shirye shiryen gwamnati na gina sababbin makarantu da asibitai da kuma gyara hanyoyi.
Johnson ya kuma sake jadada alkawarin yakin neman zabe da ya yi na gina sababbin asibitoci arba’in a Birtaniya, yace sakataren harkokin lafiya Matt Hancock zai fitar da jerin sababbin gine-ginen a cikin makwanni kalilan masu zuwa.
Ya kuma yi alkawarin kara yawan kudin da ake kashewa kan kiwon lafiya da kuma yiwa tsarin kula da lafiya garambawul da aka gaza yi cikin shekaru 30.