Birnin Madrid Zaiyi Baki Wannan Mako - 21/4/2014

Birnin Madrid zai samu kanshi a tsakiyar duniyar kwallon kafa a cikin makonnan, inda yake karbar bakoncin Bayern Munich domin karawa da Real Madrid, ita kuma Atletico Madrid, Chelsea zata yiwa maraba a wasannin kusa da karshe na Champions League.

Pep Guardiola da Jose Mourinho kamar yadda kowa ya sani sun share shekaru masu yawa a can Spain suna wasanni iri iri, kafin Guardiola yayi kaura sannan Mourinho ya bishi shima ya bar Spain.

Yanzu dai Kwaca-kwacen zasu koma birnin Madrid, inda kungiyar Mourinho wato Chelsea take karawa da Atletico Talatannan, shi kuma Gouardiola da tawagarshi ta Bayarn suke dira a Madrid larabannan domin yin wasannin zagayen farko na wasannin kusa da karshe.

A halin da ake ciki dai yanzu, akwai kofuna 14 tsakanin wadannan malaman guda biyu, ana bude idanu da kunnuwa domin ganin yadda zata kaya tsakanin Madrid da Bayarn, to ko meyasa? Guardiola fa ba’a taba cinyeshi ba a gidan Madrid, a wasanni bakwai da yayi a matsayinsa na Kwac din Barcalona.