Ma'aikata wadanda suke amfani da mukamansu wajen arzurta kawunansu zasu fuskanci ICPC, a wani sabon yunkuri tsarkakewa da kuma tsabtace ma'aikatan gwamnati.
Hukumar hana zarmiya da dukiyar jama'a ICPC, tace zata binciki ma'aikatan gwamnati wadnada suka arzurta, kuma babu yadda za'a yi ace albashinsu ne sarsalar dukiyarsu.
Hukumar zata duba ajiyarsu a bankuna,kadarori da suka mallaka kamar gidaje mallaka a Legas da Abuja, da wasu sassan Najeriya.
Wasu ma'aikatan gwamnati da suka bayyana ra'ayoyinsu kan wannan shiri, sun bayyana goyon bayansu, suna cewa ai irin wadannan mutane suna suka arzurta kansu ba Allah ne ya arzurta su ba. Sabo da irin son zuciyarsu ayyukan da suka kamata a yi domin moriyar talakwa hakan bai samu ba.
Wasu kuma suka ce wannan mataki zai zama ishara ga ma'aikata masu tasowa su san cewa doka ba zata bar su idan ta riske su daga irin take-takensu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5