Bincike ya nuna jemagu suna dauke da miyagun cututuka

Jemagu

Jemagu da ake samu a galibin kasashen nahiyar Afrika suna dauke da wadansu munanan kwayoyin cuta guda biyu masu kisa da yana yiwuwa su yada su ga mutane.
Jemagu da ake samu a galibin kasashen nahiyar Afrika suna dauke da wadansu munanan kwayoyin cuta guda biyu masu kisa da yana yiwuwa su yada su ga mutane. Duk da yake masu ilimin kimiyya sun san cewa, jemagun na dauke da kwayoyin cutar da dadewa, wani sabon bincike ya nuna irin munin cutar. Bisa ga binciken, sulusin jemagu suna dauke da kwayar cutar da take kama da cutar haukan kare, yayinda kashi arba'in da biyu bisa dari kuma suke dauke da kwayar cutar da ake kira henipavirus wadda take kisa.

Masu bincike a jami'ar Cambridge da kuma kungiyar kula da gandun daji ta Birtaniya sun gudanar da bincike a kan jemagu dubu biyu daga kasashen nahiyar Afrika goma sha biyu.

Sun tarar cewa kwayar halittar jemagun iri daya ce, wannan yana nufin cewa, suna tafiya su kuma yi cudanya da juna a duk fadin nahiyar. Babban jami'in wallafa rahoton James Wood daga jami'ar Cambridge yace wannan cudanyar tana kara yada kwayar cutar.

Jemagu suna zama cikin gungu daya da ke tara sama da jemagu dubu, sau da dama kusa da birane. Ana yawan farautarsu domin nama, abinda zai iya sawa su yada kwayoyin cutar. Ana kuma iya daukar kwayar cutar da ake kira Henipavirus ta wajen taba fitsari ko kashin jemage.

Ba a sami bullar daya daga cikin cututukan da jamagun ke dauke da shi tsakanin mutane a nahiyar Afrika ba, kuma yayinda ake ci gaba da bayyana fargaban yaduwar cutar, babbar jami'ar buga rahoton, Alison Peel tayi gargadi da cewa, kokarin kawar da jamagu daga birane zai iya kara hatsarin yada ta. Bisa ga cewarta, abinda ya kamata a yi shine fadakar da mutane su rika wanke hannunsu da kyau idan jemage ya cije su ko kuma suka taba jemage.