Binance Zai Dakatar Da Hada Hadar Naira Daga Dandalinsa

Crypto SEC Binance

Babban Kamfanin hada-hadar kudin crypto na Binance ya ce zai daina musayar kudin Najeriya na Naira daga ranar takwas ga wannan watan na Maris.

A cikin wata sanarwar da kamfanin na Binance ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, ya ce duk wadanda kudinsu na Naira ya rage a cikin asusunsu, zai a mayar da shi kuɗin crypto na stablecoin idan wa’adin ya cika.

Matakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin Najeriya ta tsare wasu manyan jami’an kamfanin Binance a birnin Abuja.

A makon da ya gabata ne hukumomin Najeriya suka tsare wasu manyan jami’an Binance guda biyu bisa zargin da ba a bayyana ba kuma har yanzu suna tsare a cewar lauyoyinsu.

Hukumomi na zargin Kamfanin Binance ne da aikata laifi wajen “kayyade farashin kudin kasashen waje a kasar.”

A makonnin da suka gabata ne Gwamnatin Nijeriya ta zargi Binance da taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin dala a kasar da kuma lalacewar darajar naira abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.

Darajar takardar kudin Najeriya Naira dai ta yi faduwar da ba a taba gani ba a tarihi tun bayan da Shugaban kasar Bola Tinubu ya kyale kasuwa ta tantance darajarta.

Lamarin ya kara jefa tattalin arzikin Najeriya da kuma al'ummar kasar cikin garari, abun da ake ganin ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

A bayan nan ne Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa “kusan dala biliyan ashirin da shida na bi ta Binance ta hanyoyin da masu amfani da manhajar ke bi, da ba za mu iya tantancewa ba”.

Gwamnan ya nuna damuwa game da shigar da musayar crypto a cikin haramtacciyar hanya a Najeriya.