Bill Gate ya zai bada ladan dala dubu dari biyar ga jihohin da suka shawo kan cutar Polio a Najeriya

Kiwon Lafiya

Gidauniyar tallafi ta Bill da Milinda Gates ta sanar da bada ladan dala dubu dari biya ga jihohin da suka iya shawo kan cutar shan inna baki daya a jihohinsu a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

Gidauniyar tallafi ta Bill da Milinda Gates ta sanar da bada ladan dala dubu dari biya ga jihohin da suka iya shawo kan cutar shan inna baki daya a jihohinsu a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

Shirin da aka ba lakabi “Kalulabar shugabancin gwamnoni a fannin rigakafi” da aka kirkiro tare da hadin guiwa da taron hadin kan gwamnonin, zai yabawa gwamnonin da jihohinsu suka cika sharudan da aka gindaya na rigakafin wanda zai kai ga shawo kan cutar shan inna ko kuma Polio.

Za a ba jihohin da suka cika sharudan kyautar dala dubu dari biyar daga gidauniyar Bill da Milinda Gates da nufin mara bayan yunkurinsu na biyan muhimman bukatun jihohin na kiwon lafiya.

Sanawar ta bayyana cewa, shugabannin Najeriya suna da kyakkywar rawar da zasu iya takawa wajen shawo kan cutar shan inna a Najeriya yayinda Gidauniyar Bill da Milinda Gates tayi alkawarin tallafawa wajen shawo kan wannan cutar da ake iya magancewa.