An yi zaben shugaban kasar Amurka a watan Nuwamban bara kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada duk shekaru hudu hudu inda aka zabi Donald Trump na jam'iyyar Republican. Haka kuma al'ada ta tanada cewa bikin rantsar da shugaban sai ranar 20 ga watan Janairu na sabuwar shekara.
WASHINGTON DC —
Kamar yadda tsarin mulki ya tanada za'a rantsar da Shugaban Amurka ranar Juma'a 20 ga watan Janairu, ranar da Donald J. Trump zai zama shugaban kasa ya kama madafin ikon kasar.
Shi ma Michael R. Pence zai dare kan kujerar mataimakin shugaban kasa bayan an rantsar dashi.
Wa'adin shugaban kasa zai fara da karfe goma sha biyu bayan da alkalin alkalan kotun koli ya rantsar dashi.
An shirya bukukuwa iri-iri bayan rantsuwar da su kade-kade da raye-raye na musamman a cikin birnin Washington DC da kewaye.