Duniya Na Bikin Ranar Yancin Yan Jarida

Wani rahoto da aka fitar na shekara da kungiyar yan jarida ta Reporters without boarders ta wallafa, na nuni da cewa cin zarafin yan jarida da ake yi na cigaba da karuwa, ba kawai a kasashen da ake mulkin mallaka ba.

Yayin da duniya ke bikin ranar yancin yan jarida yau, yan jaridu a fadin duniya na fuskantar barazanar kuntatatawa, kame, wasu ma har ya kai a kashe su saboda aikin su kawai. Yayinda jerin kasashen da suka fi takunkunmi bai sauya ba, sabbin barazana kan yan jaridu na kara fitowa daga abokan tarrayar su. Kungiyoyin kare yancin sun ce yancin yan jarida na kara shiga hadari, a maimakon ingantuwa.

Amurka ta koma matsayi na 45 a jerin. kungiyar RSF ta kira Donald Trump ''mai yawan son cin zalin yan jarida'' wanda ya sha kiran yan jarida makiyan al'umma. Kungiyar ta ce kamen yan jarida ya karu a shekara da ta gabata.

Muna ganin alakar cin zarafin ta baka kan yan jarida daga shugaban da cin zarafi a fili a anan. Amma muna ganin tasirin da hakan ke da shi a fadin duniya kan battuwan da ya shafi yancin aikin jarida.

Bisa ga cewar Freedom house, yancin aikin jarida a duniya yayi kasa sosai a shekaru 13. Kashi 13 cikin 100 ne kawai ke jin dadin aikin jarida.