Takwas ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin nazari kan irin nasarori da mata suka samu a sassan duniya da kuma kalubalen da suke fuskanta.
Ko da yake, an dade ana bikin ranar ta mata, amma sai a shekarar 1975 Majalisar Dinkin Duniya ta rungumi wannan rana a hukumance.
Taken wannan shekara shi ne “kwadaitar da jama’a” wajen mayar da hankalinsu kan al’amuran da suka shafi saka mata a harkokin yau da kullum.
Muhimman batutuwan da akan tabo a wannan rana da ake binkinta a kowace shekara, sun hada da kawar da matsalar nunawa mata wariya, cin zarafinsu da kuma tabbatar da daidaito a tsakanin maza da mata.
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya zukulo wasu daga cikin hotunan yadda aka gudanar da bikin a sassan duniya. A sha kallo lafiya: