Amirka da Cuba suna zargin juna da keta hakkin jama'a

Sakataren harkokin wajen Amirka yana yin hannu da yan kasar Cuba a birnin Havana

Yanayin murna daya kewaye daga tutar Amirka a ofishin jakadancinta a birnin Havana kasar Cuba ya buge da zama musayar zarge zarge da kakausan harshe tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka Jonh Kerry da takwaran aikinsa na kasar Cuba Bruno Rodriguez akan batun kare hakki da 'yancin jama'a.

Yanayin murna daya kewaye daga tutar Amirka a ofishin jakadancinta a birnin Havana kasar Cuba nan da nan ya canja ya buge da zama musayar zarge zarge da kakausan harshe tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka Jonh Kerry da takwaran aikinsa na kasar Cuba Bruno Rodriguez akan batun kare hakki da 'yancin jama'a.


Musayar kalamomin da aka yi ya nuna a filli cewa a yayinda kila an bude kafar da kasashen biyu zasu tattauna sabanin dake tsakanin su, magance su zai zama da wuya, gurguwa da auren nesa.


A saboda matsin lamba daga masu hankoron kare hakkin jama'a da masu hamaiya anan Amirka, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya jaddada wannan batun a wajen taron yan jarida na hadin gwiwa da takwaran aikin sa na Cuba bayan bikin daga tutar Amirka a ofishin jakadancinta a birnin Havana da aka yi jiya Juma'a.

Mr Kerry yace abubuwa zasu fi yiwa Cuba kyau idan ta kafa mulkin democradiya, inda mutane zasu samu 'yancin zaben shugabaninsu da baiyana ra'ayinsu da bin addinin da suke so ba tare da tsangwama ba.


Shi kuma takwaran aikinsa na Cuba Bruno Rodriguez yace mai dokar barci baya gyangyadi, ya maida martani inda shima ya la'ani yadda yake kare hakki da yancin jama'a nan Amirka. Musamma ma yayi misali da abubuwan da suke faruwa tsakanin yan sanda da bakar fata, inda yace, yan sanda suna kashe bakar fatar da basu dauke da wani makami.

Ya kuma yi misali da yadda Amirka take amfani da gidan yarin Guantanamo Bay wajen tsare wadanda aka kama da suna yaki da ta'adanci har sai abinda hali yayi. Mr Rodriguez yace ba'a nuna bambamcin launin fata a kasar Cuba, kuma yan sanda basu musgunawa jama'a kasar sa.


To amma sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya musunta wadannan zarge zarge a tattaunawar da yayi da yan jarida daga bisani yana mai fadin cewa al'amari kamar kashe matashi bakar fata Micheal Brown a Ferguson jihar Missouri, al'amari ne da manufar gwamnati bata amince dashi ba.