Bikin Baje Kolin Kayan Kawa Na Masu Nakasa

Your browser doesn’t support HTML5

A sassan duniya musamman a kasashe masu tasowa wasu kan nuna tsangwama ga mutane masu nakasa ta hanyar nuna cewa ba za su iya gudanar da wasu ayyuka kamar mutane masu lafiya ba.
A Malawi, mutane masu nakasa, dake sana’ar kayan kawa sun dade suna gwagwarmaya da batun wariya da ake nuna musu. Don shawo kan wannan matsalar, wani kamfanin kayan kawa a Malawi, House of Xandria ya shirya bikin baje koli na farko a kasar na mutane masu nakasa. Ga fassarar rahoton Lameck Masina daga Blantyre.