Don haka, abin da ke faruwa yanzu na ayukkan ‘yan fashin daji, asalinsa baya rasa nasaba da abin da ya faru a wancan lokacin.
Wannan bayanin yana zuwa ne lokacin da ake ta lalaben hanyoyin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaye Najeriya ta hanyar bitar ayyukan magabata musamman na daular Usmaniya wadda Fulani suka assasa.
Tarihi ya nuna cewa bayan da aka kammala jihadin kafa daular Usmaniya karkashin jagorancin Shehu Usmanu Danfodiyo, Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya yi kokarin kakkafa garuruwa domin hada jama'a wuri daya a zaman wani tanadi na samar da rundunonin k-ota-kwana, inda ya umurci Fulani da su dawo cikin gari sai aka samu rabuwar kanunan Fulanin zuwa gida uku.
Dr. Aliyu Usman Tilde wani bafulatani mai yawan bincike da rubuce rubuce a kan lamurra da dama kuma yanzu kwamishinan ilimi a jihar Bauchi ya bayyana cewa kashi biyu daga cikin Fulanin ne suka bi umurnin Sarkin Musulmi, Muhammad Bello, yayin da kashi na uku ya fandare.
Bayanai sun nuna cewa Fulanin da suka zabi zama daji sune ke yawon kiyo daga kasa zuwa kasa tun a wancan lokacin amma kuma duk da hakan suna bayar da gagarumar gudunmuwa wajen habaka tattalin arzikin lardunan lokacin saboda kudaden jangali da suke bayarwa.
Fiye da shekaru 200 yanzu da kafuwar daular Usmaniya wadda ke da cibiyar ta a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, ko baya ga rubuce rubuce da wadanda suka assasa cibiyar suka yi, haka ma an samu wasu sun yi rubuce rubuce a kan cibiyar, kamar marubucin tarihin nan na Afirka Farfesa Murry Last, wanda ya yi rubutu a kan cibiyar duk domin jagora ga jama'a a kan rayuwa da ayyukan magabata wadanda kuma ba zasu rasa tasiri ba wajen walwale wasu matsaloli irin wadanda magabatan suka hadu dasu.
To sai dai daya daga cikin daliban farfesa Murry Last, farfesa Mukhtar Umar Bunza kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar kebbi ya ce yana da kyau malaman tarihi su kara zakulo wasu bangarori da rubuce rubucen baya basu tabo ba koda zasu kara taimakawa ga magance matsalolin zamani.
Daidai lokacin da khalifan Mujaddadi shugaban majalisar koli a kan lamurran Musulunci a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar, ke cika shekaru 15 bisa halifancin wannan Talatar 2 ga wannan watan Nuwamba, masana na ganin cewa da za'a yi cikakken amfani da rubuce rubucen da magabata suka yi, da zasu iya taimakawa wajen shawo kan wasu matsalolin da suka addabi al'ummomi a wannan lokacin.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5