Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga kokarin Najeriya na samun kujerar dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya (unsc).
A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoban da muke ciki, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afrika a tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tuggar, wanda yayi tsokaci a kan hirar ta tsawon minti 30, ya yi karin haske game da matsayar ta Biden.
“Shugaba Biden ya bayyana karara cewar bai ga dalilin da Najeriya ba za ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ba,” a cewar Tuggar, inda ya jaddada muhimmancin samun goyon bayan Shugaba Biden.
Tattaunawar ta dace da mahawarar da ake cigaba da yi game da wakilcin kasashen Afrika a Majalisar Dinkin Duniyar.
“Amurka na da aniyar ganin Afrika ta samu kujerun dindindin guda 2 a majalisar,” a cewarsa.
Fatan Najeriya na samun kujerar dindindin na nuna dadaddiyar bukatar kara samun wakilci a harkokin gudanarwar duniya.
A halin yanzu, Afrika nada kujerun karba-karba guda 3 a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyar mai mambobi 15, yayin da a duk bayan shekaru 2 babban zauren majalisar ke zabar mambobin da ba na dindindin su 5 na wa’adin shekaru bibiyu.