Al'ummar yankin kudu maso gabashin Najeriya su na mayar da martani kishiyoyin juna kan wasu labarun da suka bazu a karshen makon nan, inda aka ambaci kungiyar tabbatar da kafuwar kasar Biafra ta MASSOB tana ikirarin cewa wannan abu da suke hankoro ya kusa ya tabbata.
Wakilin Muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, ya tattauna da wasu mazauna yankin wadanda ke cewa sun gwammace zama a cikin Najeriya, idan har za a tsara abubuwa ta yadda za a rika yin adalci ga kowa da kowa. Yace idan ba za a iya ba kuwa, to abu mafi alheri shine a bar su su kafa kasarsu ta Biafra.
Sai dai kuma wani dan yankin mai suna Ekwerechi Maduga yace koda yake bai san inda aka kai a game da batun kafa Biafra ba, yayi imani da cewa ko ba dade ko ba jima za a kafa ta.
Wani mai fashin baki Malam Abdullahi Rigasa, ya fadawa wakilin namu cewa za a ci gaba da samun irin wadannan kiraye-kiraye na neman ballewa muddin dai ba a kawo daidaito a kasa ba, musamman ma dai bai ma kowane dan kasa hakkinsa.
Ga cikakken rahoton nan...
Your browser doesn’t support HTML5