Bello Matawalle Na PDP Ya Zama Gwamman Jihar Zamfara

Bello Matawalle Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

Bello Matawalle Zababben Gwamnan Jihar Zamfara

Yanzu dai dan takarar babbar jam’iyyar adawa PDP a jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara.

Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya baiyana haka bayan taron nazartar hukuncin kotun koli ne da hukumar zaben INEC ta yi da ya kai ga aiyana dukkan kuri’un da APC ta samu a matsayin wadanda ba su da amfani.

Kakakin hukumar zaben Aliyu Bello ya yi karin bayanin da jaddada cewa hukumar ta na mutunta umurnin kotu ne.

A ranar litinin din nan hukumar zaben za ta mika takardar shaidar nasarar zabe ga Matawallen Maradun.

Kazalika PDP ta lashe dukkan kujerun majalisar dokokin jihar in ka debe guda daya da wata sabuwar jam’iyyar adawa NRM ta samu.

Masu sharhi na ci gaba da duba sakamakon hukuncin na kotun karshe da nuna wannan sabon babi ne a lamarin siyasa da karfafa gudanar da zaben fidda gwani ta hanyar da ta dace.