Belgium Ta Nemi Afuwar Congo Kan Mulkin "Danniya" Da Ta Yi Mata

Sarki Philippe Na Kasar Belgium

Sarki Philippe na kasar Belgium ya nuna takaicinsa kan shekara 75 da kasarsa ta yi tana mulkar Jamhuriyar Dimnokradiyyar Congo mulkin da Belgium din ta samu damar wawure arzikin kasar.

Sarki Philippe ya yi wadannan kalamai ne a jiya Talata yayin da kasar ta Congo ke bikin cika shekara 60 da samun ‘yancin kai.

Cikin wata sanarwa da ya aikewa shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi, Sarki Philippe, ya ce, “ina mai nadama bisa irin muzgunawar da aka muku a baya, wacce ake fama muku mikinta a irin abubuwan da ke faruwa a wannan zamani.”

Ita dai wannan sanarwa ta kasance hakuri na bayan-bayan nan da wani Sarkin Belgium da ke kan karagar mulki ya bayar.

A wata sanarwa da ta aikawa kamfanin dillancin labaran AFP, Ministar harkokin wajen Congo Marie Ntumba Nzeza ta ce, wannan wasika da Sarkin na Belgium ya rubuta za ta “sanyaya zuciyar al’umar kasar ta Congo,” tare da kara dankon dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A shekarar 1960 kasar ta Congo ta samu ‘yancin kai, bayan kwashe shekara 52 tana karkashin mulkin mallakar Belgium, kana ta kwashe shekara 23 tana ci gaba da zama karkashin mallakin kasar a zamanin shugaba Leopold duk da cewa an ba ta ‘yancin kai inda aka rika kwashe arzikin kasar da suka hada da roba, farin karfe, lu’ulu’u, zinare da sauran albarkatun kasa.

Miliyoyin ‘yan Congo ne suka mutu yayin da kasar ke karkashin mulkin Belgium.