Bazoum Mohamed Na Jin Kamshin Kujerar Shugaban Kasar Nijar

Bazoum Mohamed, dan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS

Yayin da jama'ar Jamhuriyar Nijar ke dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi, bayanai na nuni da cewa, tsohon ministan cikin gida Bazoum Mohamed ne ke gaba a kidayar kuri'un da ake yi.

Wakilin Muryar Amurk a Yamai ya ruwaito cewa an kammala kidayar mafi aksarin kuri’un da aka kada inda mai yi wa ake tunanin za a fitar da sakamakon zaben a yinin Talata.

A lokacin hada wannan rahoto, shafin yanar gizon hukumar zabe ta CENI ya nuna cewa Bazoum na da kuri'a miliyan 2,020 590 yayin da Mahamane Ousmane na RDR na da kuri’a miliyan 1, 476 257 – amma ba a kammala kidayar ba.

“Ana iya cewa an ma zarce kashi biyu cikin uku na yawan da’irori da ake da su a wannan kasa.” In ji wakilin Muryar Amurka, Souley Moumouni Barma.

An dai gudanar da zaben ne a zagaye na biyu, bayan da a zagayen farko da aka yi watan ranar 27 ga watan Disamba, dukkan ‘yan takara 30 da ke neman kujerar shugaban kasar suka gaza samun kashi 50 da doka ta tanada.

Bazoum ya samu kashi 39 da dan doriya a lokacin yayin da Ousmane ya samu sama da kashi 17.

Ita dai hukumar zabe ta CENI na da hurumin fitar da sakamakon wucin gadi ne kawai, amma ba ta da ikon sanar da wanda ya yi nasara.

Za ta mika sakamakon zaben ne ga kotun tsarin mulkin kasar wacce za ta duba sakamakon ta tantance sai ta sanar da sakamakon.

To a gefe gouda kuma hukumar ta CENI ta bayyana cewa an kai harin kwantan-bauna akan wasu jami’anta a garin Dogo da ke yankin jihar Diffa.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutum guda yayin da aka raunata wasu dama dama a lokacin da jami'an ke kan hanyarsu ta kai akwatunan zabe.