Shugaban Barcelona Josep Bartomeu ya tabbatar da cewa kungiyarsa na sha'awar kawo 'dan wasa Paul Pogba daga kulub 'din Juventus.
A wasan na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na Firimiya Lig, Pogba ya yayi karon batta da babban kulob din na Spaniya Barcelona amma bai iya kare kulub 'din sa na Juventus ba daga ci 3 – 1.
Koda shike kulob din na Barca bazai iya karbar sa hannun bakin ‘yan wasa ba har sai watan janairu na shekarar 2016, amma shugaban kulob din Bartomeu ya nuna matukar ra’ayin sa akan dan wasan na France International.
“da gaske ne cewar Pogba na daya daga cikin babbar bukatar mu kuma muna ra’ayin sa, amma a halin yanzu bazan ce komi ba” a hirar shugaban da mujallar Telefoot.
“an haramta mana horar da sabbin ‘yan wasa har sai watan Janairu dan haka bazan ce komi ba dangane da hakan”.
An lura sa’adda Daraktan ‘yan wasan na Barca Ariedo Braid ke Magana da wakilin Pogba, Mino Raiola kafin wasan sun a karshe a Berlin, amma babban daraktan Juventus Giuseppe Marotta ya nace cewa dan wasan baza shi ko ina ba. “matsayin sa na daban ne. Pogba yana samun kwangila daga kulob daban daban kuma kara yawa suke daga shekara zuwa shekar, kuma muna bukatar goggagun ‘yan wasa domin ciyar da ‘yan wasan mu gaba.
Dan haka bukatar mu ta ta’allaka da dama akan dan wasan, kuma muna da rahotanni masu nagari dan haka baza mu sayar da dan wasan ba.
Bamu da wani shiri kan haka kuma bamu da ra’ayin sayar da shi dan haka baza mu fara wata Magana kan hakan ba, a cewar sa.