Bayyana Halin Da Shugaba Buhari Yake Ciki Shine Mafi A’ala.

  • Ladan Ayawa

Buhari

Ya kyautu ace Najeriya ta koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya

Gaskiya ni tunanen da nake yi shine mun taba shiga cikin irin wannan kangin wanda kuma ga bisa abinda ke faruwa yanzu tamkar bamu koyi darasi akan sa ba.

Dr Usman Mohammed nena cibiyar nazarin harkokin demokaradiyya yake wannan kalamin sailin da suke tattaunawa da Ladan Ibrahim Ayawa game da rashin Lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari

Na farko dai ciwo na jikin ko wane bil adama, kuma kowa da irin sanadin da ALLAH zai kira shi, kome akwai sila sabo da haka mun taba shiga cikin irin wannan hali wanda akai ta boye-boye ana ta maganganu iri-iri wanda ya bada damar har an kusa a samu wata matsala, akan wai wanene zai zabi shugaban kasa acan baya, kuma wadannan abubuwa da gaske sun faru da Najeriya kuma ALLAH cikin ikon sa yayi muna tsawon kwana munga yadda lamarin ta kasance.

Yanzu ALLAH ya kawo mu, ga rashin lafiyar wannan bawan ALLAH Shugaba Muhammadu Buhari, Ya dawo Ingila kuma yayi wa mutanen kasa bayani cewa likitocin sa sun umurce shi daga lokaci zuwa lokai ya rika komawa, to idan takama ya koma me yasa ba zai koma ba, tun da ya riga yazo yayi bayani.

Batu na biyu kuma shine idan wanna ciwo yayi tsanani duniya bata samu bayani ba ‘yan Najeriya basu samu bayani ba, ba yadda za ayi a samu bayani, har takai ga bada damar bada Baraka yadda har wasu zasu fito su daga kundin tsarin mulki su rika wata hayaniya, to me zai sa ba za ayi bayani ba ko kuma shi ya fito yayi bayani ba.

Sai dai da aka tambayi Dr Usman cewa bai jin cewa tunda mukarabban sa suna bayani, Hakan bai wadatar ba.

Sai yace wannan bai isa ba.

Ga dai ci gaba da tattaunawar ta Dr Usman Mohammed da Ladan Ibrahim Ayawa

Your browser doesn’t support HTML5

Bayyana Halin Da Shugaba Buhari Yake Shine Mafi A’ala.3'33