Kungiyar kwallon kafar Roma ta kasar Italiya ta sha kashi a wasan da suka yi da kungiyar Bayern Munich a karo na biyu cikin mako biyu, wanda yanzu haka yasa ana shakun babban wasansu.
Duk dai ta inda kungiyar Roma ta bullo ma abun babu yadda za’ayi su cimma kungiyar Bayern Munich.
Sati biyu da suka wuce, kungiyar Roma tayi ta cika baki, amma ita dai kungiyar Bayern na kallon su kawai, kuma sun samu nasarar yimusu ci 7 da 1 a wasan zakaru na Group E.
Amma duk da haka, sun dauki kwararan matakai wanda suka hutar da wasu fitattun ‘yan wasansu don su samu kuzarin buga wasa da kyau. Ita dai kungiyar Italiyar bata da amsar me yasa basuyi nasaraba, da kuma yadda koch, Pep Guardila ya basu mamaki a gwabzawarsu a filin wasan Allianz Arena na kasar Jamus inda da aka tashi da ci 2 da 0.