Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar tana bukatar a sake bitar hukuncin da ta yanke na ranar 13 ga watan Fabrairu, wanda ya soke zaben dan takararta na gwamna a jihar Bayelsa, David Lyon da mataimakinsa, Degi Eremionyo.
Bayan haka kotun kolin ta ci tarar Lyon da jam'iyyar APC jimillar kudi Naira miliyan 60 da za a ba wadanda aka yi kara wato PDP da gwamna Diri.
Za a iya cewa wannan shine kusan karo na farko da kotun mai taken “Kotun Allah Ya Isa” ta yanke hukunci akan irin wannan batu.
Yanzu dai jama'a sun zuba ido su ga sakamakon duba irin wannan batu da jam'iyyar APC daga jihar Zamfara ta shigar na bukatar ba dan takarar ta Shehu Mukhtar Kogunan Gusau nasara kan gwamnan da ke kan gadon mulki Bello Matawallen Maradun na jam'iyyar PDP.
Ita ma a nata bangaren jam'iyyar PDP ta shigar da bukatar bitar hukuncin da ya ture gwamna Emeka Ihedioha a jihar Imo ya kuma dora Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a kan kujerar gwmnan jihar.
Sai dai biyo bayan wadannan kararrakin jam'iyyar PDP ta nemi kotun kolin kasar ta sake bitar hukuncin da ta yanke na zaben shugaban kasa tsakanin dan takararta Atiku Abubakar da shugaba Muhammdu Buhari.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5