Kwato 'yan matan Chibok alhakin Gwamnatin Najeriya ne
WASHINGTON, DC —
Dan majalisar Amurka mai kula da kwamitin harkokin Afirka da kare hakkin biladam da lafiyar su Mr. Chris Smith da yake ziyaran Najeriya yayi wa ‘yan jarida jawabi a filin da ake yi gaggamin akan ‘yan matan Chibok.
Mr. Smith,yace ya zo Najeriya a bisa wakilcin kwamitin sa ne domin tattara bayanai da suka shafi fataucin mata a Najeriya.
Yace ya gana da ‘yan majalisun Najeriya da wadasu shuwagabanin addinai, kuma ya samu bayanai sosai saida yace an lura cewa ta’addanci na karuwa a duniya maimakon raguwa duk da kokarin da akeyi wajen magance shi.
Mr.Smith yace zai mika rahoton sa ga kwamitin su bayan ya koma Amurka domin nazari,amma yace alhakin kwato ‘yan mata na gwamnatin Najeriya ne.

Your browser doesn’t support HTML5