Bayan Takaddama Tsakanin Majalisa Da Fadar Shugaban Kasa Gaskiya Ta Yi Halinta - Hon Abubakar Lado

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta ba fadar shugaban kasar Najeriya goyon baya dari bisa dari a kan yaki da cin hanci da rashawa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban kwamitin labarai na majalisar Sanata Aliyu Sabe Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a Minna, ya ce hasali ma, majalisar dattawance ta bada goyon bayan gwamnati ta samar da asusun ajiya na banki guda daya da hakan yasa lamarin ya yi tasiri.

Tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Musa, ya ce daman rashin fahimata yasa ake ganin kamar sanatocin na kokarin takawa shugaba Muhammadu Buhari Burki.

Shima dan majalisar wakilan Najeriya, Hon Abubakar Lado Suleja, ya ce bayan takaddamar da aka yi ta samu tsakanin ‘yan majalisar da fadar shugaban kasa, daga bisani gaskiya ta yi halinta.

Da hukumomi a matakai daban daban ke jawabi albarkacin zagayowar ranar mulkin farar hula a Najeriya, dan majalisar wakilai Abdullahi Idris Garba, ya bayyana cewa ya taimakawa matasa daga yankinsa da kayan koyon sana’o’i na sama da kudi Naira Miliyan Tamanin domin rage zaman banza a tsakanin matasan.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayan Takaddama Tsakanin Majalisa Da Fadar Shugaban Kasa Gaskiya Ta Yi Halinta - Hon Abubakar Lado