Tsohon dan wasan Kungiyar kwallon kafa na Tottenham Roberto Soldado, ya kasance daya daga cikin 'yan wasa biyar da aka dakatar a wasan da aka fafata tsakanin Galatasaray da Fenerbahce.
Sakamakon wata hatsaniya da ta kaure tsakanin mambobin kulob din biyu inda sukayi ta ba hammata iska a wasan da aka tashi 2-2.
Soldado, mai shekaru 33, da haihuwa wanda ya shiga Fenerbahce daga Villarreal a shekara ta 2017, yana daya daga cikin 'yan wasa uku, kuma an dakatar dashi na tsawon wasanni shida.
Ku Duba Wannan Ma Cristiano Ronaldo Yace Kungiyarsa Ba Tayi Rawar Bakin HantsibaShi kuwa dan wasan Fenerbahce Jailson Siqueira, an dakatar dashi a wasanni takwas sai Badou Ndiaye na Kungiyar Galatasaray wanda aka dakatar dashi na wasanni biyar.
Shi kuwa jagoran Kungiyar Galatasaray mai suna Faith Terim, an haramtamasa tsayuwa akan layi na wasanni 7 sakamakon cin mutumcin alkalin wasa da yayi, haka kuma mataimakin sa Hasan Sas dukkansu na wasanni 8.
Dan wasan tsakiya na Galatasaray Garry Mendes Rodrigues, da takwaransa Ryan Donk an dakatar dasu wasanni uku ne da kuma wasanni shida.