Saka Bayahude cikin wadanda zasu tsayawa shugaban masu fafutikan neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ya sa Muryar Amurka ta nemi fashin baki daga yankin da ya fito da kuma lauya.
A bayanin da Onarebul Chinedu Offor, dan majalisar dokokin jihar Imo yayi yace shi belin kansa sakamakon matsin lambar gwamnonin jihohinsu ne na kudu maso gabashin kasar kan gwamnatin tarayya da fannin shari'a.
Yace Nnamdi Kanu nada magoya da yawa musamman matasan Igbo wadanda suke ganinsa tamkar jaruminsu dake yi masu fafutika. Sau tari sun sha karawa da jami'an tsaro. Belin zai kawo maslaha.
Akan cewa ya kawo Bayahude cikin wadanda zasu tsaya masa, Onarebul Chinedu Offor cewa yayi tun can farko Nnamdi yace shi ba Kirista ba ne shi kuma ba Musulmi ba ne. Yahudanci shi ne addinisa saboda haka a ganin mai shari'a ya kamata ya kawo wani daga addinisa da zai tsaya masa.
Shi ma Barrister Gambo Abdulsalami yace babu dokar da tace kotu ba zata iya saka wani sharadi ba kafin ta bada beli sai dai kada ya zama mai tsauri yadda shi mai neman belin ba zai iya cikawa ba.
A cewarsa babu abun da zai hana kotu tace Nnamdi ya kawo Bayahude ya tsaya masa saboda shi bai san cewa babu yahudawa a Najeriya ba.
Yace shi Nnamdi Kanu din yace shi bayahude ne saboda haka akwai yahudawa 'yan Najeriya, ke nan za'a samu bayahude dan Najeriya ya tsaya masa beli.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5