Masu iya magana kance “Tantabara Uwar Alkawari” Tantabara wata irin hallittace da Allah ya yi wadda take da wasu abubuwa da babu wani nau’in tsuntsu dake da shi, baya ga kyan sura da Allah yayi ma hallitar tantabara.
Tsuntsaye ne masu basira, ga tsafta da kan yi sabo da mutane, baya ga irin alkawari da suke dashi ta rikon abun alkhairi ko na sharri da aka yi musu a wuri, wanda hakan kan sasu sake ko rashin ziyartar wajen a karo na biyu.
A duk lokacin da mutum ya kalli Tantabara zaiga wata baiwa da Allah ya yi akan tsuntsayen, domin kuwa a duk cikin jinsin tsuntsaye babu tsuntsu da ke da abubuwan mamaki kamar tantabara na wajen yadda take gudanar da mu’amalarta da jinsin mutane.
Wani marubuci Mr. Bill McKenna, wanda ya kwashe shekaru 10 yana bibiyar hallayar Tantabaru, wanda ya bayyanar da cewar sune tsuntsaye da a lokacin da suke koto kuma suna iya hangen duk wani abu da yake kusa da su hara wanda yakai nisan milliyoyin kilomitoci.
Yanayin idon su da Allah yayi musu ya banbanta da irin yadda na sauran hallitu suke ko yadda suke ganni abubuwa a duk nau’in kala da duk wani abu yake. A duk lokacin da tantabara take tsakurar abinci babu wani abu da zai iya kusantar ta don cutar da ita.
Tantabara na daya daga cikin tsuntsaye da basa dauke da kowane irin cuttuka wanda kan yadu a tsakanin su ko su kai ga halittar dan adam, ya kara da cewar tantabaru kanyi wanka a kowace rana sau biyu zuwa ukku, ko ma fiye da hakan a duk lokacin da suka samu dama.
Nau’in abinci da mutane ke ciyar dasu yana taimaka musu wajen samun kuzari, girma da samun damar haihuwa akai akai.