A Bauchi Wasu Sun Mayar da Martani Akan Furucin Obasanjo

Chief Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya

Cikin wannan makon ne tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya gaza a mulkinsa yana mai shawartarsa da kada ya sake tsaya wa takara a zaben badi.

'Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani na goyon baya da akasin haka, kan kalaman tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, inda ya nemi shugaba Buhari da kar ya nemi wa'adi na biyu.

A jiya Talata Obasanjo ya fitar da wata rubutacciyar sanarawa da ya raba wa manema labarai.

A cewar Alhaji Isa Dan Masanin Minna matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki sun samo asali ne a zamanin shugabancin Obasanjo, wadanda suka hada da cin hanci.

Shi kuwa Alhaji Isa waiwaye ya yi, yana mai cewa, a zamanin shi Obasanjo ya dauki kudi ya mikawa 'yan majalisa domin su goyi bayan shirinsa na son ya zarce a mulki a wa'adi na uku.

ya kara da cewa, dangane da wutar lantarki, ya bannata kudi sama da biliyan 30 amma ba'a samu wutar ba yana mai cewa, game da layin dogo ba'a yi komai ba a lokacin mulkinsa.

Inji Alhaji Isa bai kamata ya ce Shugaba Buhari ya gaza wurin yaki da cin hanci saboda tsananin cin hanci a lokacinsa ko kasashen waje basu yadda da gwamnatin Obasanjo ba.

Sai dai yayin da wasu ke sukar shawarar Obasanjo ga Buhari, wasu na ganin shi Obasanjon ya yi daidai.

Comrade Garba Tela, ya ce a halin da ake ciki Shugaba Buhari ya tsufa ana neman canji ne yanzu.

"Ya kamata Shugaba Buhari ya koma gefe ya barwa matasa kasar.

Domin jin cikakkun martanin bangarorin biyu, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:

Your browser doesn’t support HTML5

A Bauchi Wasu Sun Mayar da Martani Akan Furucin Obasanjo - 3' 39"