Tawagar kwararru su goma sha biyar dake nazarin muhalli karkashin jagorancin Farfesa Solomon Balogun, masani a Jami’ar Wisconsin, Madison ta kasar Amurka sun bayyana cewa yanayin muhallin jihar Bauchi na daya daga cikin mafiya kyau a Najeriya, wanda zai zama abin koyi a duk fadin kasar.
Wannan yabo an yi shi ne a wajen bikin kaddamar Cibiyar Gudanar da Binciken Ruwa da Iska da Tsire-tsire da Abinci.
Taron kaddamar da cibiyar Binciken ya samu halartar masana yanayin muhalli da kuma kungiyoyin masu rajin kare muhalli a ciki da kuma wajen jihar Bauchi. Mallam Samaila Bima, shi ne shugaban kungiyar Jewel Enviromental Iniative a Najeriya kuma ya yi tsokaci kan yadda yanayin Muhalli yake a shiyyar arewa maso gabas da kuma dalilan da yake kai ga jiha ta zamo mai tsafta, wanda wadannan dalilan su ka sa Bauchi ta zama mai tsafta.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Kauran Bauchi, shi ma an karrama shi sabili da wannan fice da ya yi kan batun tsaftar muhalli, ya ce wannan karramawar na al’ummar jihar Bauchi, ta fara ne da bayyana matsayin yadda tsaftar muhalli ta ke kafin hawansa kujerar Mulki.
Domin sanin yadda na’urar kimiyyar binciken yanayi ke aiki wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya nemi bayani daga bakin Darakta Janar na hukumar kare muhalli a jihar Bauchi, Dakta Ibrahim Umar, wanda ya yi bayani dalla dalla.
Ga Abdulwahab Muhammad da ciakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5