Batutuwan Da Taron Muryar Amurka Ya Kunsa Kan Zaben Najeriya

Grace Alheri Abdu da wani jami'in INEC a wajen taron da Sashin Hausa na Muryar Amurka ya shirya a Abuja domin zaben Najeriya 02.11.19

A ranar 16 ga watan nan nan Fabrairu ne, wato ranar Asabar, za a gudanar da babban zabe a Najeriya.

A wani yunkuri na bai masu kada kuri'a damar samun karin haske dangane da zaben, Muryar Amurka ta yi wani taro na bainar jama'a a Abuja, wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a harkokin zabe, ciki har da lauyoyi da kuma masu kada kuri'a.

A yayin taron, 'yan takara na jam'iyyu daban-daban, sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda suke ganin zaben zai gudana.

“Wannan zabe, idan an fitar da sakamako, mu dauke shi tamkar kwallo muke yi, in wannan ya ci gobe kuma wani zai dauka.” Inji shugaban jam’iyyar ADPA, Shittu Muhammadu Kabiru.

Grace Alheri Abdu, wacce ta jagoranci wannan taro, ta bayyana cewa Muryar Amurka za ta ci gaba da gabatar da labaru na wannan zabe tun daga yin zaben a ranar Asabar har zuwa ba da sakamakon zaben.

“Maksudin shirya wannan taro shi ne mu kafar yada labarai ne kuma mu abin da mu ke yi shi ne ilmantar da mutane kan duk abin ke faruwa, musaman a ba da dama a kara fahimtar abin da ya shafi wannan zabe.” Inji Grace.

Wannan taro dai da Muryar Amurka ta yi shi ne kusan karo na uku da aka yi irinsa, wanda ya samu halartar jama’a da dama.

Na farko an yi shi ne tare da matasa, wadanda suka shafi masu kada kuri'a da masu sauraro, na biyu kuma da mata, sai kuma wannan daya samu halartar masu ruwa da tsaki na harkar zabe a tarayyar Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Abubuwan Da Taron Muryar Amurka Ya Kunsa Kan Zaben Najeriya - 2'24"